Insane
Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na goma sha uku

Sayyed Zakzaky2

Idan maziyyi ya fito wa wanda ya ke da alwala, ina makomar alwalarsa?
TAMBAYA: Ina hukuncin wanda ya sanya yaro dan shekara 9 ko 10 ya karya azuminsa?

Daga Maryam Ibrahim Funtuwa

SHAIKH ZAKZAKY: Idan yana nufin Uba ya tilasta ma dansa ya ci abinci ne alhali ya shekara 9 ko 10, to sai mu ce lallai ya yi laifi, kodayake su wadannan, takalifin azumin bai hau kansu ba. Amma in za su iya yi ya kamata a kyale su, sai dai in an ga azumin zai cutar da su ne.



TAMBAYA: Namiji mai mata biyu, shin shi ne ke da hakkin ba kowacce lokacin saduwa ko sai sun nema?

Daga Zainab Ibrahim Funtuwa.

SHAIKH ZAKZAKY: Abin da aka sani shi ne akwai abin da ake ce ma rabon kowace mace a daurar kwana hudu tana da kwana daya. Amma wannan ba yana nufin saduwa ba, in jima'i yake nufi da saduwa din. Shi saduwa daidai gwargwadon bukatar kawannen su ne. Hakkinsa ne hakkinta ne, saboda hakkinsu ne su biyu, bai kebanta da ita ba, bai kebanta da shi ba, tsakaninsu ne. Kuma shi rabon kwana ba lallai yana nufin jima'i bane.

TAMBAYA: Shin mutum zai iya hada Azahar da la'asar sannan ya yi nafilolinsu 16?

Daga Tukur Rufa'i Getso Gwarzo Kano

SHAIKH ZAKZAKY: Abin sani dai shi ne ana yin nafilolin zawwal kafin azuhur ne, raka'a 8. Sannan kuma bayan an yi azuhur sai a yi nafilolin la'asar raka'a 8. Amma in wani dalili ya sa an bi shi bashi, yana iya biya bayan la'asar ko ma bayan isha. Amma ba wai 'ihtiyaran' ba. Ba 'ihtiyaran' ya zama dama haka yake yi bisa zabin kansa. Kamar yadda shi a nan yana nufin cewa musamman sai ya hada azuhur da la'asar sannan ya zo daga baya ya zo da nafilolin, in ya yi haka nan kamar ya yi wani abin da ba shi aka sani ba, in dai ba wata lalura ce ta sanya, kamar kurewar lokaci, masalan. Sai ya zo da la'asar ya jinkirta nafilolin zuwa wani lokaci.

TANBAYA: Da watan azumi na ji a cikin wa'azi an ce duk wanda ya yi wa Allah laifi kuma yake neman gafarar Allah, to ya yi tuba gami da tawassuli da Imam Aliyu Ridah (AS). Don haka nan sai na ci gaba da yin tawassuli da Imam din. Shin ina iya in ci gaba da yi?

Daga Tukur Rufa'i Getso Gwarzo Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To (shi dai) tawassuli ba a kayyade shi da wani Imami kebantacce ba. Tawassuli dai yana nufin kana rokon Allah ne kana gama shi da bayin Allah nagargaru.

TAMBAYA: Ina tambaya ne game da falalar zikiri kamar yadda ya zo a Arba'una Hadith na Imam Khomaini. Shin falalar ta takaita ne ga wanda ya yi zikirin Khasatan ko har da wanda ya yi don neman biyan bukata?

Daga Husaini Aliyu Fudiyya Alkaleri Bauci.

SHAIKH ZAKZAKY: Shi dai zikiri yana nufin tuna Allah ne sabanin gafala ga barinsa. Kuma jimlar abubuwan da suka shiga duk tuna Allah, sun shiga cikin zikr, musamman salla da karatun Alkur'ani da addu'o'i da tasbihohi da tahmidodi da sauransu. Saboda haka in mutum yana da wata bukata wajen Allah, ya gabatar da sallah sannan ya yi wata addu'a ta neman biyan bukatarsa, shi ma zikr ne. Kuma addu'ar ma in mutum ya roki Allah ya ba shi wani abu, ko ma wannan abin na duniya ne mutukar bai haramta a bidi wannan abin ba, shi ma ya yi zikr ne ai.

TAMBAYA: Abu ne ya shiga tsakanin Uba da 'yarsa har ya kai matsayin ga ya tsine mata, kuma har ya ce ko ya mutu kada a ba ta gadonsa. To idan ya mutu shi kenan gadon ya haramta a gare ta ko kuwa?

Daga Husaini Aliyu Fudiyya Alkaleri Bauci.

SHAIKH ZAKZAKY: Lallai matukar 'yarsa ce, wannan rabo ne da Allah (T) ya riga ya yi. Saboda haka tana da gadonta, shi bai isa ya fitar da ita daga gadon ba. Gado Allah (T) ne ya raba ba iyaye ne suke rabawa ba.

TAMBAYA: Ya matsayin azumin mai ciwon ULCER? Zai ciyar ne ko zai rama idan azumin ya warke? Daga Fatima Kaduna.

SHAIKH ZAKZAKY: Da ma ramuwa zai yi sai dai idan ciwon ya zarce da shi har ya zuwa wani azumi ba tare da ya warke ba, ko kuma ba a sa tsammanin ma wani Ramadan ya zo alhali yana da lafiya. Wato ana tsammanin ci gaban ciwon, an tabbatar da haka nan, to sannan zai koma ma tun asali ya zama ciyarwa maimakon ramuwa. Amma abin sani shi ne mai ciwo yana biya ne in ya warke; in kuma Ramadan ya sake cimmasa ba ta tare da ya warke ba, shi kenan ramuwa ta fadi a kansa sai ya koma ga ciyarwa.

TAMBAYA: Meye hukuncin sukuwar dawaki wanda akan sa wata kyauta ga wanda ya yi na daya?

Daga Shehu mai Burodi

SHAIKH ZAKZAKY: To in dai shi bai sa kudi ba, shi wanda ya shiga takarar, to ya halasta. Amma in su masu takarar ne suka zuba kudi, dayansu ya ci, to ta zama caca.

TAMBAYA: Muna so a taimaka mana da hakikanin fassarar ayar nan da take cewa; "mazinaci ba ya aure face mazinaciya, haka mazinaciya ba ta aure face mazinaciЕ"Har ya zuwa karshen ayar.

Daga Ayuba mai gyaran wuta Karkasara da Ahamad Tela Kasuwar Barci Kaduna

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, to aure a nan ya zo da ma'anarsa ne na luga, wato ainihin zinar ake nufi kenan. Wato saduwar namiji da mace shi ne aka kira aure. Wato ka ga shi mazinaci ba zai yi jima'i da wata ba ta fuskacin zinarsa in ba ita ma irinsa ce mazinaciya ba. Haka nan kuma ita ma mazinaciya ba za ta sami wanda za ta iya yin zina da shi ba sai dan uwanta mai ra'ayi irin nata, mazinaci. Wato aure a lugga yana nufin shigar wani abu a wani abu ne. Kuma a wannan ma'anar aka yi amfani da shi a nan.

TAMBAYA: Batun ayar da ta hana Bani Isra'ila kamun kifi ranar Asabar. Shin har yanzu wannan ayar tana aiki?

Daga Sa'eed Ya'u Mijinbir Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To duk shari'o'in Manzannin da suka gabata, shari'ar wannan Manzo namu ya riga ya shafe ta. Saboda haka in dai Ba'isra'ile yana nan yanzu ko da zai ga sahihiyar Attaurar Musa, in ya bi ba za a karba masa ba saboda an aiko da hukuncin da ya shafe wadancan hukunce-hukunce. Allahumma sai dai in ba shi da labarin aiko Manzon Allah, to sai ya zama yana kan wannan abin nasa, to za a iya amsa masa. Amma ban sani ba ko akwai wadansu mutane yanzu da suke addinin Yahudu da Nasara alhali ba su da labarin an aiko Manzon Allah, in dai akwai su to suna da hujja. Sai mu ce gare su wannan ayar tana nan tana aiki; in akwai su!

TAMBAYA: Mahaifin Imam Ali Abi Dalib shi ne sunansa kenan ko alkunyarsa ne?

Daga Sa'eed Ya'u Mijinbir Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To lallai sunansa ne. Kuma dai abin da ya shahara da shi kenan, ba a san ana kiran sa da wani abu ba banda Abu dalib din.

TAMBAYA: Meye hukuncin mutumin da yake shan hannu da abokin kasuwancinsa wanda ba musulmi ba?

Daga Salisu Kano Walawa Kano.

SHAIKH ZAKZAKY: In musafaha yake nufi, to ba wani abin da ya hana yin musafaha da wanda yake ba musulmi ba, sai dai idan hannunsa da jibi, zai lizimta wa mutum wanke hannu saboda rashin amintuwa da tsarkakar wannan hannun nasa da ganin cewa su ba su san meye najasa ba da meye mai tsarki ba. Amma idan hannuwan nasu busassu na guda biyu babu komai.

TAMBAYA: Ina hukuncin wanda yake sayar da gwanjo sai ya wanke su ya sa masu sitati su yi karfi don jawo hankalin masu saye?

Daga Salisu Kano walawa Kano

SHAIKH ZAKZAKY: Babu laifi in masu sayen sun fahimci cewa gwanjo suke saye. Sai dai in ya yi masu yaudara, ya nuna masu cewa sababbi ne, kamar ya sa su a cikin leda sai su fito a matsayin sababbi, to shi ne zai zama ya yi yaudara kenan. Amma matukar su masu saye sun san gwanjo suke saye, to babu laifi.

TAMBAYA: Shin ina matsayin cin abinci da wanda ba musulmi ba, ko wanda ba musulmin ba ya ci ya rage?

SHAIKH ZAKZAKY: To lallai akwai daukar wulakanci a ciki, kuma abin da duk za ka yi ya zama ya wulakanta matsayin musulmi da Musulunci dole ka bar shi. In dai da daukar wulakanci. Allahuma sai dai bisa ta fuskacin lalura.

TAMBAYA: Mutane na cewa wai in talauci ya dame ka, to ka kara aure. Yaya wannan hadisin?

Daga Musa Shukrah Karmo Abuja

SHAIKH ZAKZAKY: To ban san me ya sa ya ce masa hadisi ba? Tunda mutane ne suke cewa, sai ya ce ya fadin wadannan mutanen? Sai in ce kila su mutanen al'adarsu ce ko camfinsu. Amma dai cewa hadisi, ba gaskiya ne ba. Ko da akwai wani abu da suka kira shi hadisi, to ba shi da wani tushe

TAMBAYA: Mutum ne matarsa ta mutu tana bin sa bashi har N1500. Shin yaya zai biya ta?

Daga Jibril Dingim Munjibir Kano

SHAIKH ZAKZAKY: To zai biya bashin ne a yayin da za a raba gadonta. In ma babu, sai ya sanar da cewa tana bin sa bashi, alabashi tunda yana da gadonta kila kason ya fada a abin da shi zai gada, sai ya zama ba sai ya biya ba kenan.

TAMBAYA: Mutum ne bayan ya gama sallah yana sauraren wata sallar sai maziyyi ya fito masa. Yaya alwalarsa?

SHAIKH ZAKZAKY: To ai maziyyi ba shi daga cikin abubuwan da suke warware alwala. Yana da kyau mutum ya karanta babin abubuwan da ke warware alwalla ya gani a cikin 'Risala amaliyyan

.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din